Fatan alheri daga malam Usman Abba Agaji Gashua, Nijeriya
Muna mai taya ku murnar shiga sabuwar shekara ta 2013. Hakika ya zama dole mu yaba wa sabuwar kasar Sin ta zamani bisa babbar moriya da gwamnatin jama'ar Sin da Sinawa a dangane da sa kaimi da kuke kare martaba da kima da tagomashin kasashenmu na Afirka masu tasowa a duniya. Lalle kam, kasar Sin tana nan daram a matsayinta na wanzar da zaman lafiya mai daurewa a kasashenmu na Afirka masu tasowa da ma duniya baki daya. Duk lokacin da wata hatsaniya ko rigima ta barke a wata kasa a nahiyar Afirka ko ma a wata kasa a fadin duniya baki daya, kasar Sin ta kan ce a kasashen su warware matsalarsu ta hanyar daurewa teburin sulhu da matakan diplomasiyya. Yanzu sabuwar kasar Sin ta riga ta yiwa sauran kasashen duniya zarra da fintinkau wajen saurin bunkasuwa da samar da zaman lafiya a duniya, masamman a kasashenmu na Afirka masu tasowa.
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku