DAN WASAN KULAF DIN SYRIANSKA DAKE KASAR SWIDEN YUSUF SALEH, NA CIKIN 'YAN WASA 3 MASU TAKA LEDA A KETARE DA KASAR HABASHA ZATA YI AMFANI DASU YAYIN GASAR CIN KOFIN NAHIYAR AFIRKA DAKE TAFE
A yayin da ake ci gaba da shirye shiryen fara gasar cin kofin kwallon kafar nahiyar Afirka. Kuloflikan kasashe 16 da zasu taka leda yayin gasar na ci gaba da bayyana jerin 'yan wasan da za su shiga gasar tare da su, tare da bayyana ragowar muhimman batutuwan da suka shafi kulaflikan nasu. Ga misali mai horas da 'yan wasan kasar Habasha Sewnet Bishaw ya bayyanawa manema labaru cewa, dan wasan kulaf din kasar Swedin Yusuf Saleh mai shekaru 28 da haihuwa, na cikin jerin 'yan wasa 23 da za su wakilci kasar a gasar ta bana, kuma yana cikin 'yan wasan kasar 3 dake taka leda a manyan kulaflikan kasashen waje. Ragowar 'yan wasan sune Saladin Seid dake wasa a kungiyar Wadi Degla ta kasar Masar, da kuma Winger Fuad Ibrahim dake kulaf din Minnesota Stars dake Arewacin Amurka.
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku