in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar AU ta ce, ta zaku ta warware rikicin jamhuriyar demokiradiyar Congo
2013-01-08 10:09:13 cri

Kwamishinan kungiyar AU mai kul.a da wanzar da zaman lafiya da tsaro Ramtane Lamamra, ya ce, kungiyar ta zaku ta zakulo hanyar warware rikicin da ke faruwa a gabashin jamhuriyar demokiradiyar Congo.

Jami'in ya bayyana hakan ne ga manema labarai a ranar Litinin, jim kadan bayan ya gana da shugaban kasar Ruwanda Paul Kagame a ofishinsa da ke Kigali, babban birnin kasar.

Ya jaddada cewa, rikicin da ake fuskanta a gabashin jamhuriyar demokiradiyar Congo, na bukatar kulawa ta musamman, kuma AU ta zaku ta lalubo hanyar magance wannan matsala daga tushe.

Ramtane ya ce, "Yayin ziyarata, na samu zarafin ziyartar cibiyar tsugunar da 'yan gudun hijira ta wucin gadi da ke kan iyakar Ruwanda da jamhuriyar demokiradiyar Congo, kuma na tattauna da mutane don kimanta yadda al'amura ke gudana."

A ranar Jumma'a ne Lamamra ya ziyarci Ruwanda daga jamhuriyar demokiradiyar Congo a wata ziyarar kwanaki 4 da ya kai yankin, bugu da kari ya ziyarci kan iyakar Burundi da Ruwanda don duba yanayin tsaro a wurin.

Yayin rangadin nasa, jami'in na AU ya kuma gana da wasu manyan jami'ai daga bangaren jamhuriyar demokiradiyar Congo da Ruwanda don tattauna yanayin da ake ciki a manyan tabkunan da ke shiyyar wato Great Lakes, a wani bangare na kokarin da ake na tunkurar rikicin jamhuriyar demomiradiyar Congo.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China