Tun daga ranar 4 ga wata ne, Madam Lagarde ta fara ziyarar aiki na kwanaki biyu a kasar Malawi inda a lokacin wani dandalin tattaunawar da aka shirya ta yaba wa gwamnatin kasar Malawi bisa ga kyawawan sakamakon da ta samu a cikin aikin gyare-gyaren tattalin arziki da take gudanarwa, wanda ya maido da odar tattalin arzikin kasar yadda ya kamata.
Madam Lagarde ta kuma yi fatan ganin Malawi za ta ci gaba da inganta wannan aiki, sannan raya tattalin arzikinta a fannoni daban daban a maimakon dogaro bisa ayyukan gona kawai.
A nata bangaren, shugabar kasar ta Malawi Joyce Banda ta yi alkawarin cewa, ko da yake aikin gyare-gyare yasa jama'ar ta cikin wani halin kunci, duk da haka gwamnati ba za ta yi watsi da wannan shiri ba domin ana sa ran ganin farfadowar tattarlin arzikin kasar a karshen wannan shekarar da muke ciki.(Kande Gao)