Mukaddashin Darekta na shiyyar mulki na hukumar yada labarai da buga takardu Jiang Jianguo a lokacin wani ganawa da ma'aikatan hukumomin yace ta kokarin nuna kansu a kasuwannin gida ,gidajen yada labarai da buga takardu su yi kokarin shiga fagen da za'a taka rawa da su a kasashen duniya yadda ya kamata kuma su himmatu wajen kafa rassa da buga labaran su a kasashen waje ta hanyar sayen hannayen hannun jari da wassu hanyoyi da ya kamata.
A cewar Mr Jiang hukumar za ta ba da goyon baya ga manyan hukumomin buga takardu domin su shiga fagen da za'a dama da su a kasuwannin duniya sannan kuma za ta goyi bayan shaharrarun marubuta da kungiyoyi domin su samu su fadakar da duniya game da al'adun Sinawa.
Jiang wanda ya bukaci kafofin yada labarai da buga takardu da su ja ra'ayin masu karatu ta hanyar mai da hankali a kan wassu kungiyoyi na musamman da buga labarai masu bambanci da saura, ya kuma jaddada cewa kwaskwarima wajen ayyuka, a mayar da kungiyoyin da gwamnati ke daukar nauyin su a kamar su kungiyar raye raye da raya al'adun gargajiya da kuma gidajen buga takardu, zuwa kungiyoyin da za su nemi kudi da kansu domin su dauki nauyi in sun ci riba ko in sun fadi. (Fatimah)