Kasashen Ivory Coast, da Ghana, Cape Verde, Africa ta kudu, da Angola, na cikin wadanda 'yan wasan su zasu baje basirar su yayin gasar. Ragowar kasashen sune Morocco, Niger, Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo, da Zambia. Sai kuma Nigeria, da Burkina Faso, da Algeria, Tunisia da Mali da Habasha da kuma Togo. Kamar dai yadda tuni hukumar kwallon kafa ta duniya ta bayyana hakan.
A halin da ake ciki wadannan kungiyoyin kasashe sun riga sun gudanar da wasannin sada zumunta, a wani mataki na share fagen tunkarar kalubalen dake gaban su.
A shekarun baya a kan iya bayyana kasashe mafiya karfi da ka iya lashe wannan gasa, amma a baya bayan nan mawuyacin abu ne kai tsaye a bayyana wasu kasashe kalilan a matsayin zakaru, duba da yadda kasashe daga ko wane fanni na wannan nahiya ta Afirka ke bayyana kwazon su yayin wannan gasa. Ya dai isa misali ganin yadda yayin wannan gasa data gabata, kasar Zambia ya lashe kofin, bayan dauki ba dadi da aka yi tsakanin ta da kasar Ivory Coast. Duk kuwa da manyan 'yan wasa dake taka leda a manyan kulaflikan duniya dake tawagar kungiyar ta Ivory Coast, irin su Didier Drogba, da Kolo Toure, Didier Zokora da dai sauran su.
Ganin yadda wannan gasa ke cigaba da karatowa tuni manazarta harkokin wasan kwallo suka fara furta albarkacin bakin su, tare da hasashen irin kungiyoyin da ka iya yin rawar gani. Cikin tambayoyin da ake yi kuwa akwai shin ko ita kasar Zambia dake rike da kambun wannan gasa zata iya kare shi? Ko kuwa kasar Ivory Coast da ta zo ta biyu za ta yunkuro ta sauya tarihin gasar, musamman ma ganin yadda shekarun manyan 'yan wasanta sun fara ja, ga shi kuma wannan kofi ya kufce daga hannun ta tun a shekara ta 2006. A hannu guda kuma akwai kasar Afirka ta kudu da ke matsayin mai masaukin baki, shin ko wannan kasa tana da wani shiri na ganin ba a zo garinta an fita rawa ba?.
Wadannan dai kadan ne daga irin tambayoyin da masu kallo zasu amsa bayan da aka fara taka leda, kamar dai yadda masu iya magana kan ce, ba a san maci tuwo ba, sai miya ta kare.
Batu filayen wasa kuwa akwai filaye 5 da suka hada da na birnin Johannesburg: Soccer City (94,000 capacity)
Durban: Moses Mabhida Stadium (54,000)
Nelspruit: Mbombela Stadium (41,000)
Port Elizabeth: Nelson Mandela Bay Stadium (48,500)
Rustenburg: Royal Bafokeng Sports Palace (42,000)
Dangane da jadawalin wasannin kuwa, an shirya fara buga kwallo cikin wannan gasa ranar 19 ga watan Janairun nan, kamar dai yadda muka ambata, inda ake sa ran bude gasar da wasa tsakanin kasar Afirka ta kudu da Cape Verde, da kuma wasan Angola da Morocco a ranar farko wato 19 ga wata a filin wasa na Johannesburg. Wannan dai wasa zai zamo na farko a gasar, kuma na farko cikin jerin wasannin rukuni na farko wato rukunin A.
Ragowar wasannin dake tafe suna.
Group A
South Africa v Cape Verde 1600 (agogon Afirka ta Kudu), Angola v Morocco 1900
Jan 23
South Africa v Angola 1500, Morocco v Cape Verde 1800
Jan 27
South Africa v Morocco 1700
At Port Elizabeth
Cape Verde v Angola 1700
Group B
(Port Elizabeth unless noted)
Jan 20
Ghana v DR Congo 1500, Mali v Niger 1800
Jan 24
Ghana v Mali 1500, Niger v DR Congo 1800
Jan 28
Ghana v Niger 1700
At Durban
DR Congo v Mali 1700
Group C
(Nelspruit unless noted)
Jan 21
Zambia v Ethiopia 1500, Nigeria v Burkina Faso 1800
Jan 25
Zambia v Nigeria 1500, Burkina Faso v Ethiopia 1800
Jan 29
Zambia v Burkina Faso 1700
At Rustenburg
Ethiopia v Nigeria 1700
Group D
(Rustenburg unless noted)
Jan 22
Ivory Coast v Togo 1500, Tunisia v Algeria 1800
Jan 26
Ivory Coast v Tunisia 1500, Algeria v Togo 1800
Jan 30
Ivory Coast v Algeria 1700
At Nelspruit
Togo v Tunisia 1700
Quarter-finals
Feb 2
At Port Elizabeth
(1) Gp B winners v Gp A runners-up 1500
At Durban
(2) Gp A winners v Gp B runners-up 1830
Feb 3
At Rustenburg
(3) Gp D winners v Gp C runners-up 1500
At Nelspruit
(4) Gp C winners v Gp D runners-up 1830
Semi-finals
Feb 6
At Durban
Winners quarter-final 2 v winners quarter-final 3 1500
At Nelspruit
Winners quarter-final 4 v winners quarter-final 1 1830
Third place
Feb 9
At Port Elizabeth
Semi-finals losers 1800
Final
Feb 10
At Johannesburg
Semi-finals winners 1800