Wani jami'in tsaro da kuma kamfanin dillancin labaran kasar Masar MENA sun bayyana jiya Lahadi 30 ga wata, cewar a kalla mutane 2 aka kashe sannan wasu guda 2 suka samu rauni sakamakon harin bom da aka kai wa wata majami'ar kibdawa ta Masar a garin Misrata dake yammacin kasar Libya, wadanda dukkansu 'yan kasar Masar ne.
Jami'in ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua cewa, wasu maza da ba'a san ko su waye ba su ne suka wurga ababen fashewa da ake kerawa a gida a majami'ar dake Misrata, wanda ke da nisan kilomita 200 gabas da Tripoli, babban birnin kasar Libya.
A halin da ake ciki, faston majami'ar ya ce, mutane 3 ne suka samu rauni sakamakon tashin bom din, inda daya daga cikinsu ya mutu sakamakon raunin, sannan ginin majami'ar ya lalace baki daya.
Kafofin watsa labaran kasar sun bada rahoto cewa, wani jami'in ofishin jakadancin kasar Masar dake Tripoli Hatem Abdel Qader ya ce, sauran mutane 2 sun bar asibiti a ranar Lahadi cikin kyakkyawan yanayi. Haka kuma ya kara da cewa, mahukuntan kasar Libya na binciken al'amarin. (Lami)