in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Christopher Katongo ya zama dan wasan kwallon kafa mafi hazaka na Afirka da aka zaba a BBC
2012-12-27 15:53:59 cri
Bisa labarin da gidan rediyon kasar Ingila wato BBC ya bayar, an ce, Christopher Katongo mai shekaru 30 ya sami galaba ne akan Demba Ba, da Didier drogba, da Younes Belhanda, da kuma Yaya Toure, a wannan gasa ta zabar dan kwallon kafa mafi hazaka na nahiyar Afirka, kuma dan wasan farko daga yankin kudancin nahiyar da ya cimma wannan nasara ta karbar lambar yabo da kafar yada labaru ta BBC ke gudanarwa, .

Masana daga kasashen nahiyar Afirka sun gabatar da jerin sunayen 'yan takara a zaben da BBC ya yi. A karshe, Katongo ya samu kuri'u fiye da kashi 40 cikin dari.

A watan Febrairun bana, Katongo ya taimaki kungiyar kasarsa ta Zambia wajen shiga gasar cin kofin Afirka, inda kungiyar sa ta doke kungiyar kasar Cote d'Ivoire da mashahurin dan wasa Didier Drogba ya jagora ta hanyar bugun daga ka sai mai tsaron gida.

A ganin BBC, idan Katongo ya ci gaba da gwada kwarewa a kungiyar kasarsa ta Zambia, karfin kungiyar zai dada inganta zuwa wani sabon matsayi. A kuma gabar da ake hangen karatowar gudanar gasar cin kofin duniya a kasar Brazil cikin shekarar 2014, ana dakon ganin ko Katongo zai ci gaba da jagorantar kungiyar kasar ta Zambia, wajen samun kyakkyawan sakamako. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China