Yaya Toure ya cimma nasara a zaben dan wasan kwallon kafa mafi hazaka na nahiyar Afirka a bana

A ranar 21 ga wata a birnin Accra dake kasar Ghana, hukumar kula da harkokin wasan kwallon kafa ta nahiyar Afirka CAF, ta gudanar da bikin bada lambobin yabo, inda aka gabatar da sakamakon zaben dan wasan kwallon kafa mafi hazaka na nahiyar Afirka a bana, inda dan wasa daga kasar Cote d'Ivoire Yaya Toure wanda kuma ke takawa kungiyar Manchester City ta kasar Ingila leda, ya lashe zaben, don haka ya zama dan wasan kwallon kafa mafi hazaka na Afirka a wannan shekara ta 2012. Yaya Toure ya zamo zakara a wannan lokaci ne tsakankanin manyan 'yan wasan nahiyar ta Afirka irin su takwaran sa Didier Drogba.
Cikin dai manyan nasarorin da wannan dan wasa ya cimma a bana akwai taimakawa kungiyar sa ta Manchester City cimma nasarar lashe gasar Premier.
Koda yake shima Didier Drogba ya jagorinci kungiyarsa ta Chelsea wajen lashe gasar zakarun Turai, kana ya zama dan wasa mafi kyau wato MVP a gasar, amma a zaben dan wasan kwallon kafa mafi hazaka na nahiyar Afirka a bana, Yaya Toure ya fi samun kuri'u masu yawa.
Bayan da Yaya Toure ya cimma nasarar zaben, ya bayyana cikin farin ciki cewa, wannan dare ya zama na musamman gare shi. Domin wannan ne karo na biyu a jere da ya samu wannan lambar yabo. (Zainab)