Drogba ya bayyana aniyar sa ta ci gaba da taka leda a kungiyar Shenhua ta kasar Sin
A 'yan kwanakin baya, dan wasan kwallon kafa na kasar Cote d'Ivoire Didier Drogba, ya karbi lambar yabo ta dan wasa mafi kyau a kungiyar Chelsea, da masu sha'awar kungiyar suka zaba. Drogba ya bayyanawa 'yan jarida cewa, ba zai manta da shekaru 8 da ya shafe yana bugawa tsohuwar kungiyar tasa wasa ba, koda yake dai ya ce, yana matukar jin dadin taka leda a sabon kulob din sa na birnin Shanghai dake nan kasar Sin, kuma yana fatan zai ci gaba da yin wasa a kungiyar da ake kira Shenhua ta birnin Shanghai yayin kakar wasanni mai zuwa.
Drogaba ya bayyanawa 'yan jarida cewa, wannan lambar yabo ya dauke ta da matukar muhimmanci, kasancewar ta an bada ita gareshi, duk kuwa da cewa shi dan wasa ne daga ketare, a cewar sa hakan ya nuna irin tarin nasarar da ya samu cikin wadancan shekaru 8. Ya kuma ce yayin da yake taka leda a kungiyar, ya koyi abubuwa da dama, ya kuma yi cudanya da manyan 'yan wasa da yawa.
Bayan dai kammala gasar wasan kwallon kafa ta kasar Sin ta bana, Drogba na can cibiyar horo ta kungiyar Chelsea, yana kuma ci gaba da shirye shiryen tunkarar gasar nahiyar Afirka dake tafe. (Zainab)