Inda a wannan karo, za ta yi wasa da ragowar kungiyoyi masu karfi ciki hadda Super Eagle ta Nijeriya a rukuni C, inda kasar ta Zambia ke fatan kara cimma nasara a gasar a wannan karo.
Bayan da aka kawo karshen kakar wasanni ta wasan kwallon kafa ta kasar Sin, dan wasa daga kasar Mali dake taka leda a wata kungiyar kwallon kafa ta kasar Sin wato Seydou Keita bai huta ba, inda a yanzu haka yake can birnin Barcelona, domin ci gaba da shirye shirye share fagen gasar cin kofin na nahiyar Afirka da za a gudanar a shekarar badi. Kungiyar sa ta kasar Mali wadda a gasar data gabata ta samu matsayi na uku, a wannan karon ita ma za ta taka leda da kasashe irin su Nijer, da Congo Kinshasa, da kuma Ghana a cikin rukuni na B.
Ban da wannan kuma, a halin da ake ciki an riga an kira mashahurin dan wasa nan Gervais Yao Kouassi, na kungiyar Arsenal ta kasar Ingila domin bugawa kungiyar sa ta gida wato Cote d'Ivoire, ya kuma fara shirin share fagen taka kwallo a gasar cin kofin na nahiyar Afirka. Kungiyarsa ta Cote d'Ivoire za ta murza kwallo da Tunisia, da kasar Algeria da kuma Togo a runkuni na D.
Za dai a fara gudanar da gasar cin kofin na nahiyar Afirka na shekarar 2013 ne daga ranar 19 ga watan Janairu mai kamawa, zuwa ranar 10 ga watan Febrairu ranar da ake fatan kammala gasar a birnin Johannesburg, babban birnin kasar Afirka ta kudu. (Zainab)