A jiya dai dubu-dubatan mutanen kasar Masar sun mamaye tituna domin nuna kiyayya wassu kuma don nuna goyon baya kan kada kuri'a. Bugu da kari, a wannan rana, an yi taho mu gama tsakanin magoya baya da masu adawa da shugaba Mohamed Morsy a birnin Alexandria dake dab da tekun Bahar Rum.
Sojojin kasar sun shirya sosai domin tabbatar da jefa kuri'ar raba gardama lami lafiya inda kawo yanzu kimanin sojoji dubu 120 da motocin yaki dubu 6, ciki har da tankoki, suna zaman ko ta kwana.
Sai dai yanzu ana damuwa kan wasu harkoki, misali, har yanzu ba a samu isassun alkalai wajen sa ido kan jefa kuri'ar raba gardama. Ko da yake kwamitin yanke shari'a a matsayin matakin koli na kasar Masar ya riga ya amince da alkalai da su shiga wannan aiki, amma wasu alkalai sun nuna kiyayya kan wannan batu. A sakamakon karancin yawan alkalai masu sa ido, dole ne ya sa aka raba aikin kashi biyu, wato bayan da aka kammala jefa kuri'a a ranar 15 ga wata, za a ci gaba da jefa kuri'a a zagaye na biyu a ranar 22 ga wata.(Fatima)