Alexandre Song, dan wasa daga kasar Kamaru ya bugawa kungiyar Arsenal wasa ne a gasar Premier a karon da ya gabata. Kuma duk da cewa kungiyar tasa ba ta cimma nasarar lashe gasar ba, amma duk da hakan Song ya nuna kwarewar sa yayin da yake taka leda a gasar. Don haka, kungiyar Barcelona ta saye shi a kakar wasanni ta bana.
Shi kuwa Didier Drogba, mashahurin dan wasa ne daga kasar Cote d'Ivoire, wanda yake wasa a wata kungiyar kwallon kafa ta garin Shanghai dake nan kasar Sin , ya sake shiga zaben dan wasan kwallon kafa mafi kwarewa na Afirka ne a wannan shekarar ta 2012, a matsayin sa na dan wasa mai tarihin gaske. Da farko, dai ya taimaki kungiyar Chelsea wajen lashe gasar zakarun Turai. Kana ya jagori kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar sa wato Cote d'Ivoire, yayin wasan karshe na cin kofin kasashen nahiyar Afirka, wadda ya gabata, wanda kuma kasar Zambia ta lashe, bayan da aka kai ga bugun daga kai sai mai tsaron gida. Don haka, kafofin watsa labaru na kasa da kasa suna ci gaba da nuna kyakkyawan fata ga Drogba. Idan Drogba ya cimma nasara, zai zama dan wasa na hudu da ya shiga kundin tarihin 'yan wasa mafiya hazaka da suka samu wannan matsayi har sau 3 a nahiyar ta Afirka.
Ban da Song da kuma Drogba, Yaya Toure daga kasar Cote d'Ivoire shi ma ya shiga zaben a bana. Yaya Toure ya bayyana kwarewarsa a kungiyar da yakewa wasa wato Manchester City, ya kuma taimaki kungiyar wajen cimma nasarar kasancewa zakara a gasar Premier ta bana, don haka ya shiga takara a zaben na bana.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, za a gabatar da sakamakon zaben a ranar 20 ga watan Disamba nan a birnin Accra dake kasar Ghana. (Zainab)