Bayan karin yini daya, a karshe dai an tabbatar da wa'adi na biyu na takardar Kyoto bisa dokoki, da cimma daidaito kan hadin gwiwa wajen sa kaimi ga gudanar da yarjejeniyar cikin dogon lokaci, da bin tsarin daukar nauyin daya amma da bambanci, da kiyaye tsarin yarjejeniyar da takardar Kyoto, wadanda suka kasance sakamako mafi muhimmanci da aka samu a taron na Doha.
A gun taron, a bayyane kasashe masu sukuni suka yi yunkurin rage nauyin dake kansu na tarihi da kuma tsarin daukar nauyi daya amma da bambanci, ba su son rage fitar da gurbatacciyar iska a kasashensu, da zuba jari da samar da fasahohi ga kasashe masu tasowa. Wannan zai kasance wata babbar matsala da kasa da kasa za su fuskanta wajen hadin gwiwa kan tinkarar matsalar sauyawar yanayi a nan gaba.
A matsayin wata kasa mai tasowa da kuma daukar alhaki, kasar Sin ta halarci dukkan shawarwarin da aka yi a taron Doha cikin yakini, tare da taka rawar a zo a gani a fannoni daban daban a gun taron.(Fatima)