Jami'ar Liaoning ta Sin da jami'ar Dakar ta Senegal ne suka hada kai wajen kafa wannan kwaleji. Jakadar Sin da ke kasar Senegal Xia Huang, wakilin ministan ma'aikatar kula da harkokin aikin koyarwa na jami'o'i Amadou Tidiane Guiro, shugaban jami'ar Liaoning da kuma na jami'ar Dakar da dai sauran wakilan fannoni daban daban na kasashen biyu kimmanin dari biyu sun halarci bikin.
A yayin wannan biki, jakada Xia Huang ya nuna cewa, tun lokacin da kasar Sin da kasar Senegal suka sake kulla dangantakar diflomasiyya tsakaninsu, kasashen biyu sun karfafa musaya da hadin gwiwa a fannin al'ada. Kafuwar kwalejin koyar da Sinanci ta Confucius a kasar Senegal za ta zurfafa musayar al'ada tsakanin kasashen biyu, kuma za ta ba da taimako wajen kara fahimtar juna tsakanin al'ummomin kasashen biyu tare kuma da samun ci gaba tare.
Amadou Tidiane Guiro ya nuna cewa, sakamakon da kasar Sin ta samu wajen fannonin kimiyya da fasaha, samar da isasshen abinci, kawar da talauci da dai sauransu sun zama abubuwan koyi ga kasashen Afirka. Kafuwar kwalejin koyar da Sinanci ta Confucius a jami'ar Dakar ba ma kawai za ta ba da taimako ga musayar al'adun harsuna ba ne, za ta kuma ciyar da nazarori tsakanin kasashen biyu kan ayyukan koyarwa, ilimomi da nazarin kimiyya da fasaha gaba. (Maryam)