A ranar 27 ga wata da safe ne aka dauki samfuri daga gawar marigayi Yasser Arafat da aka tono daga kabarinsa da ke yammacin gabar kogin Jordan, kuma a wannan rana da yamma, gwamnatin Palasdinu ta kira taron manema labarai, inda Abdullah Bashir, mamba a kwamitin binciken musabbabin mutuwar Yasser Arafat ya bayyana yadda aka dauki samfurin da kuma yadda za a gudanar da binciken kamar haka, "kamar yadda aka shirya, kwararru masu bincike na Palasdinu sun dauki samfurin da da suke bukata bisa sanya idon kungiyoyin bincike uku a wurin, wadanda daga baya za su gudanar da bincike a dakunan gwaje-gwajen da ke a kasashensu, amma a kalla za a yi wata uku kafin a samu sakamakon binciken."
A watan Yuli na wannan shekara ne, wata hukumar nazari a kasar Switzerland ta sanar da gano sinadari mai guba nau'in Polonium 210 a kayan da maragayi Arafat ke sanye da shi lokacin da ya bar duniya, abin da ya janyo bincike a game da musabbabin mutuwar marigayin. Hukumar Palasdinu bayan da ta yi tunani sosai ta yanke shawarar hako kabarin marigayin, don daukar samfuri daga gawarsa, ta yadda za a tabbatar da ko ya mutu ne sanadiyyar sinadari mai guba da ake zargin an sanya masa ko a'a.
Al'ummar Palasdinu duk da cewa suna ganin hakan ya saba wa dokokin musulunci da kuma burin marigayin, kuma ba su son ganin hako gawar marigayin, amma akasarinsu suna kuma daukan cewa, girmamawa ce ga marigayin, in dai an sake gudanar da bincike kan gawarsa don gano gaskiyar lamarin da ya faru. Wata mata da ke zama a birnin Ramallah a yayin da take tattaunawa da wakilinmu tana mai cewa,"A matsayina na 'yar Palasdinu, binciken da ake gudanarwa kan musabbabin mutuwar marigayi Yasser Arafat ya zo a makare, duk da haka abu ne mai kyau, sabo da duk wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar marigayin, ko da shugaban kasa ne, ya kamata a yi masa hukunci."
Kudurin hukumar Palasdinu ya kuma samu goyon baya daga kungiyar masu fafutuka ta HAMAS. A yayin da kakakin kungiyar, Ihab R.al-Ghusain ke tattaunawa da wakilinmu, ya bayyana cewa,"Cikin shekaru da dama da suka wuce, mun yi ta kira da a gudanar da bincike kan musabbabin mutuwar marigayi Arafat, kuma muna fatan za a samu bayani mai gamsarwa daga binciken da ake yi a yanzu haka, sabo da mun san Isra'ila ce take da hannu cikin lamarin. Wannan dai wani muhimmin ci gaba ne da aka samu, kuma ya kamata a ci gaba da yinsa, kuma a tabbatar da mai laifi."
A cewar gwamnatin Palasdinu, kungiyoyin bincike na kasa da kasa sun dauko samfurin zuwa gida, sai dai a kalla watanni uku ne za a shafe kafin a samu sakamakon binciken. Ko ma'aikatan binciken za su iya gano gaskiyar lamarin wannan shi ne abin da kowa ke zura ido a kai.
Hasali ma dai, akasarin Palasdinawa suna da imani kan cewa, marigayi Arafat ya mutu ne sakamakon kisan gillar da aka yi masa a maimakon rashin lafiya. Akwai kuma wasu 'yan Palasdinu da suka tabbatar da cewa, Isra'ila ce ta aikata kisan, ko kai tsaye ko kuma a fakaice, ita ce ta kashe marigayin. Sai dai Isra'ila a nata bangaren ta musanta zargin sau da dama. Hillel Frisch, wani masanin Isra'ila da ke nazarin huldar da ke tsakanin Palasdinu da Isra'ila, ya ce, babu wata bukata ga Isra'ila ta kashe Arafat, kamar yadda ya ce, "A ganina, ba Isra'ila ba ce ta kashe Arafat. Sabo da na tabbata kangiyar da aka yi masa ta yi aiki sosai, kuma a hakika tun da dadewa kafin rasuwar Arafat, an yi nasara a kansa, kuma Isra'ila ta ci nasarar yakar ta'addanci."
A yanzu haka, ana jiran sakamako daga kungiyoyin bincike, kuma sakamakon zai yi tasiri sosai a kan huldar da ke tsakanin Palasdinu da Isra'ila. Akwai jama'ar Palasdinu da ke ganin cewa, in dai sakamakon ya nuna cewa, Isra'ila ce ta yi wa Arafat kisan gillar, to, halin da ake ciki zai iya tabarbarewa. Amma Hillel Frisch, masanin na kasar Isra'ila yana ganin cewa, kome mene sakamakon, ba zai kawo manyan sauye-sauye ga huldar da ke tsakanin kasashen biyu ba, kamar yadda ya ce,"Idan dai har aka gano shaidar da ka iya tabbatar da zargin da ake wa Isra'ila, a ganina, Palasdinawa ba za su ta da babban rikici ba, saboda ba su da karfi da za su yaki Isra'ila."(Lubabatu)