An raba kungiyoyi 16 da suka samu damar shiga gasar cin kofin Afirka a wannan karo cikin rukunoni 4. Kasashen da suka fi karfi a cikin gasar su ne Afirka ta kudu mai karbar bakuncin gasar,sai Zambia da ta lashe kofin a yayin gasar da ta gabata, Ghana da kuma Cote d'Ivoire. Kasar Kamaru ta sha kashi a wasan da ta yi tsakaninta da kasar Cape Verde, wannan ne karo na biyu a jere da kasar Kamaru ta kasa shiga gasar cin kofin Afirka.
A gasar cin kofin Afirka na shekarar 2012, kasar Zambia ce ta zama zakara, wannan labari ya ba da mamaki sosai ga jama'ar kasashen Afirka, Zambia ta lashe Cote d'Ivoire ta hanyar bugun daga kai sai mai tsaron gida inda ta yi nasara a wasan. A wasan cin kofin Afirka a wannan karo, an sanya kasar Zambia cikin rukuni na 3 wato (C), kuma a cikin wannan rukuni, akwai Nijeriya ,Burkina Faso da kuma ta kasar Habasha.
A cewar mashahurin dan wasan kasar Cote d'Ivoire Didier Drogba, ya ji bakin ciki sosai domin kasarsa ta kasa cimma nasara a wasan karshe na gasar cin kofin Afirka da ya gabata, a wannan karo yana fatan kasarsa za ta lashe wannan kofin. Amma a wannan karo,baya ga Cote d'Ivoire, Algeria, Tunisia, da kuma Togo, sauran kasashe ukun ma suna da karfi.
Afirka ta kudu, Cape Verde, Morocco da kuma Angola suna cikin rukuni na farko wato (A). A cikin rukuni na biyu ko kuma (B), akwai Ghana, Mali, Nijer da kuma Congo Kinshasa.Yayin da Zambia, Nijeriya, Burkina Faso da kuma Habasha za su fafata a cikin rukuni na 3 wato (C). Kana a rukuni na 4 ko kuma (D), akwai Cote d'Ivoire, Algeria, Tunisia da kuma Togo. (Zainab)