in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dukkan kungiyoyi ko kasashe 16 da za su halarci gasar cin kofin kwallon kafa naAfirka ta shekarar 2013 sun fito
2012-10-25 19:35:12 cri
A kwanakin baya, an gudanar da gasar zagayen karshe na neman shiga gasar cin kofin kwallon kafa na Afirka ta shekarar 2013, wadda aka yi a tsakanin kasar Toga da Gabon. A karshe, kasar Togo ta lashe kasar Gabon da ci biyu da daya. Don haka, bayan da aka yi wasannin biyu a tsakaninsu, Togo ta samu iznin shiga gasar cin kofin Afirka ta shekarar 2013 da za a yi a kasar Afirka ta Kudu.

Ya zuwa yanzu, dukkan kungiyoyi ko kasashe 16 da za su halarci gasar cin kofin kwallon kafa naAfirka ta shekarar 2013 sun fito, kana an raba su cikin rukunoni 4. Cote d'Ivoire, Afirka ta kudu mai karbar bakuncin gasar, Zambia da kuma Ghana suna cikin rukuni na farko.Sai kasashen Mali, Tunisia, Angola da kuma Nijeriya da ke cikin rukuni na biyu. Algeria, Burkina Faso, Morocco da kuma Nijer suna cikin rukuni na uku. A rukuni na hudu kuma, akwai Habasha, Togo, Cape Verde da kuma Congo Kinshasa. Wadannan kasashe 16, sune za su halarci gasar cin kofin kwallon kafa na Afirka karo na 29 da za a fara tun daga ranar 19 ga watan Janairu zuwa ranar 10 ga watan Febrairu na shekarar 2013. Kuma wannan ne karo na farko da kasar Cape Verde ta shiga gasar a tarihi, kana kasar Habasha ta sake shiga gasar bayan shekaru 31.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China