Hukumar kula da harkokin wasan kwallon kafa ta nahiyar Afirka ta fara zaben zakarar dan wasan kwallon kafa na nahiyar ne tun daga shekarar 1993. Didier Drogba daga kasar Cote d'Ivoire ya taba samun wannan lambar yabo sau biyu a shekarar 2006 da kuma 2009. Kuma Seydou Keita daga kasar Mali shi ma ya zo matsayi na biyu a zaben lambar yabo da aka yi a shekarar bara.
A shekarar 2012, Drogba ya taimaki kungiyar Chelsea ta kasar Ingila wajen lashe kofin kwallon kafa na zakarun nahiyar Turai da gasar kungiyoyin wasan kwallon kafa na kasar Ingila wato gasar firimiya. Hakazalika, a matsayinsa na dan wasan kasarsa ta Cote d'Ivoire, Drogba ya taimaki kungiyar Cote d'Ivoire wajen zama matsayi na biyu a gasar cin kofin Afirka. Don haka, a wannan shekara, Drogba ya fi samun damar cimma wannan lambar yabo.
Hukumar kula da harkokin wasan kwallon kafa ta nahiyar Afirka za ta jefa kuri'a tsakanin 'yan takara 34 cikin jerin sunayen da ke neman samun lambar zakarar dan wasan kwallon na nahiyar a shekarar 2012, kana za su zabi 'yan takara guda 10 a karshen wannan wata bisa kuri'un da suka samu. Daga baya kuma, manyan sakataren hukumomin wasan kwallon kafa na kasashen Afirka da masu horas da kungiyoyin kasashen Afirka za su zabi mutum guda cikin 'yan takara 10 a zagaye na biyu. Kuma za a gabatar da sakamako a bikin bada lambar yabo na hukumar kula da harkokin wasan kwallon kafa ta nahiyar Afirka na shekarar 2012 a ranar 20 ga watan Disamba a Accra, babban birnin kasar Ghana. (Zainab)