Wannan ne karo na biyu da Nijer din ta shiga gasar cin kofin kwallon kafa na kasashen Afirka bayan shekarar 2011. Za a gudanar da gasar ce a wannan karo a kasar Afirka ta kudu a shekarar 2013.
A farkon rabin lokaci na wasan da aka yi tsakanin Nijer da Guinea, babu wadda ta jefa kwallo a ragar wata. Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne, Mohamed Francisco Chikoto da Boubakar Issoufou daga Jamhuriyar Nijer suka zura kwallayen da suka baiwa kasar nasara. A karshe, Nijer ta doke Guinea da ci biyu da nema
A wasan farko da aka yi tsakanin kungiyoyin biyu a kasar Guinea a ranar 9 ga watan Satumba, Nijer ce ta samu nasara da ci daya mai ban haushi. (Zainab)