A ranar Alhamis din da ta gabata ne shugaban al'ummar Falasdinu Mahmoud Abbas, ya yi wata ganawar sirri da ministan tsaron kasar Isra'ila Ehud Barak a Amman dake kasar Jordan. Kamar dai yadda wata kafar yada labarun kasar Falasdinu ta bayyana a Litinin din da ta gabata, wannan ganawa ta samu halartar Sarki Abdallah na Jordan.
Taron a cewar majiyar ya mai da hankali ne kan nemo hanyoyin da za a bi, domin sake komawa teburin shawara, don magance matsalolin dake tsakanin kasashen Falasdinu da Isra'ila, tare da shirin da Falasdinun ke yi, na neman amincewar kafuwar kasa mai 'yanci karkashin majalissar dinkin duniya.
Yayin tattaunawar dai Barak wanda shi ne jagoran jam'iyyar Labor ta kasar Isra'ila, ya bayyanawa Abbas aniyarsa ta daukar matakan janye dakarun kasarsa daga yammacin kogin Jordan, yayin da shi kuma shugaba Abbas ke nanata matsayinsa, dangane da rashin amincewa da duk wani yunkuri na cin iyakar kasar Falasdinu. Wannan dai shi ne karon farko da shugaba Abbas ya tattauna da wani babban jami'in Isra'ila, tun bayan da aka gaza cimma daidaito tsakanin yankunan biyu, dangane da batun kara gina matsugunnan Yahudawa.(Saminu)