A matsayinsa na wani gagarumin bikin cinikayya na kasa da kasa dake da dogon tahiri, da babban matsayi, kuma bisa sikeli mafi girma, kullum bikin baje koli na Guangzhou na kasancewa wani dandalin nune-nune dake jawo hankalin masana'antun cinikayyar waje a ko wace shekara. Manema labaru sun gano cewa, manyan kamfanoni kamar su Haier, Changhong, Media, da ma kanana da matsakaita, na mayar da hankali matuka wajen kafa rumfunansu, domin kara jawo hankalin masu sayen kayayyaki.
Kamfanin Haier da ya kasance kamfanin kirar kayayyakin lantarki na gida da ya fi girma a duniya, ya sanya rubutun "Global No. 1" a rumfunansa.
Jami'ar dake kula da harkar tallace-tallecen kamfanin madam Wang ta bayyana cewa, kamfanin Haier na dora muhimmanci sosai kan wannan bikin baje koli.
"Kamfanin Haier ya kafa rumfuna 54 da fadinsu ya kai muraba'in mita 500, inda za a nuna nau'oin kayayyaki sama da 260, cikin samfuri kimanin 13. Mutanen dake halartar bikin sun hada da wakilan sassanmu daban daban dake kasashen waje, da manajojin kasuwanni, wadanda yawansu ya kai kimanin 150."
Madam Wang ta kara bayyana cewa, yawan mutanen da za su ziyarci rumfuna na kamfanin Haier a ko wace rana zai iya wuce dubu 50, kuma kamfanin ya tanadi ma'aikata da dama domin biyan bukatun sabbin masu sayen kayayyakin su. Ko da yake dai masana'antun dake halartar bikin sun shirya sosai, amma matsanancin yanayi da tattalin arzikin duniya ke ciki na cigaba da sanya tarnaki. Gaban rumfa ta wani kamfani, manema labaru sun gano cewa, wasu 'yan kasuwan kasashen waje sun gamsu da kayayyakin da kamfanin ya kawo, amma yawan kayan da suke da bukatar oda ba su da yawa. Ma'aikacin kamfanin, mista Hua ya bayyana cewa, 'yan kasuwar kasashe da yawa su kan yi taka-tsantsan kafin su yi oda, gaskiya ne ana shan wuya wajen cinikayya, duk da dai kamfanin nasu na cigaba da kokarin kawar da matsalolin da ake fuskanta. Mista Hua ya ce,
"Bugu da kari karuwar darajar musayar kudin Sin, ita ma ta kawo tasiri ga 'yan kasuwa masu burin sayen kayayyaki daga kasashen waje, inda a hannu guda yawan kudin da 'yan kasuwa za su yi amfani da su wajen sayen kayayyaki a ko wace shekara bai cika canzawa ba, sakamakon hakan yawan kayayyakin da suke saye na raguwa. A irin wannan yanayi dole ne kamfani ya canza tsare tsaren sa."
A matsayinsa na wata hanyar dake bude kofa ga kasashen waje, bikin baje koli na Guangzhou ya kasance wani muhimmin dandali da kamfanonin kasar Sin ke samun oda daga 'yan kasuwar waje. Mai magana da yawun hukumar dake shirya bikin baje- kolin mista Liu Jianjun ya bayyana cewa, kamfanoni kusan kashi 50 cikin dari ne suka gaza halartar bikin, sakamakon rashin isassun rumfuna.
Liu na ganin cewa, ko da yake akwai batun tabarbarewar tattalin arzikin duniya, kuma ana fuskantar yanayi mai tsanani wajen cinikayyar waje, amma duk da haka kasar Sin ba ta rage fifikon da take nunawa ga bunkasuwar cinikayyar waje ba.
"Muna iya ganin cewa, ba a rage fifikon da kasar Sin ke nunawa kan habaka cinikayyar waje ba, a sa'i daya kuma kasar na tabbatar da fifikonta ga sabbin fannoni. Matsin lamba da kamfanoni ke fuskanta daga waje ya tilasta su kyautata tsarin masana'antu, da canja hanyoyin bunkasuwa, da kuma kara karfin takara a duniya." (Bilkisu)