in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya gana da shugaban majalisar jama'ar kasar Cape Verde
2012-09-28 21:04:41 cri
Ranar Jumma'a 28 ga wata da yamma, Wu Bangguo, shugaban majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya gana da shugaban majalisar jama'ar kasar Cape Verde Basílio Mosso Ramos.

A yayin ganawar, mista Wu Bangguo ya ce, bayan da kasashen Sin da Cape Verde suka kulla dangantakar diplomasiyya a tsakaninsu yau shekaru 36 da suka wuce, kasashen 2 na girmama juna ta fuskar siyasa, tare da yin zaman daidai wa daida, sannan suna samun fahimtar juna da mara wa juna baya kan muhimman al'ammuran da suka jawo hankalinsu, tare da yin hadin gwiwa sosai cikin al'ammuran kasa da kasa. Haka zalika kasashen 2 suna taimakawa juna da samun moriyar juna ta fuskar tattalin arziki. Sun kuma samu sakamako da dama bisa ga taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsaksanin kasashen Sin da Afirka da yin hadin gwiwa a tsakanin kasar Sin da kasashe masu amfani da harshen Portuguese ta fuskar tattalin arziki da ciniki. Har wa yau yin mu' amala a tsakanin kasashen 2 ta fuskar al'adu ya kasance sabon fanni na bunkasa dangantaka a tsakaninsu.

Mista Wu ya kara da cewa, majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na son yin mu'amalar sada zumunta da hadin gwiwa a tsakanin majalisar jama'ar kasar Cape Verde a matakai daban daban, a kokarin ci gaba da samun fahimtar juna da mara wa juna baya a kan babbar moriyar juna da kuma muhimman batutuwan da suka jawo hankalinsu, da inganta yin mu'amala da yin koyi da juna a fannonin tafiyar da harkokin kasa da kafa dokoki da sa ido da dai sauransu, da zummar kara taka rawa wajen zurfafa dangantakar abokantaka da hadin gwiwa a tsakanin Sin da Cape Verde.

A jawabinsa, mista Ramos ya ce, har kullum kasar Sin na tsayawa tsayin daka kan yin zaman daidai wa daida tare da dukkan kasashen duniya, lamarin da ya taimaka wa kasarsa ta Cape Verde, kasa mai tasowa, ta iya bayyana ra'ayinta da kuma kiyaye hakkokinta yadda ya kamata. Kasar Cape Verde na sa ran inganta mu'amalar sada zumunta a tsakanin gwamnatoci da majalisun kasashen 2 da kuma jama'ar kasashen 2, kyautata hadin gwiwar samun moriyar juna a fannonin aikin yawon shakatawa, ilmi, aikin kamun kifi, kayayyakin more rayuwar jama'a da makamantansu, a kokarin zurfafa zumuncin da ke tsakanin kasashen Cape Verde da Sin. Dadin dadawa mista Ramos ya sake nanata cewa, kasarsa na nacewa kan bin manufar kasar Sin daya tak a duniya.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China