Ranar 20 ga wata, a birnin Brussels hedkwatar kasar Bulgium, an yi ganawa karo na 15 tsakanin shugabannin Sin da Turai, da taron koli na masana'antu da ciniki tsakanin Sin da Turai a karo na 8. Shugaban majalisar tarrayar Turai (EC) Herman Van Rompuy, da shugaban hukumar EU José Manuel Barroso sun gamsu da cigaban da bangarorin biyu suka samu a cikin shekaru 10 da suka gabata, sun kuma jaddada muhimmancin dangantakar dake tsakaninsu.
A wannan rana da safe, firaministan kasar Sin Wen Jiabao da Herman Van Rompuy, da kuma José Manuel Barroso, sun jagoranci ganawar a karo na 15, bayan ganawar, mataimakin ministan harkokin waje na kasar Sin Song Tao ya bayyanawa kafofin yada labaru na Sin da kasashen waje ci gaban da aka samu a gun ganawar.
Song Tao ya ce, firaminista Wen Jiabao ya nuna cewa, tsarin tattaunawa tsakanin shugabannin Sin da Turai na da amfani matuka, kuma yana fatan kasashen Turai sun dauki matakin da ya dace, don warware batun hana sayarwa kasar Sin makamai, da kuma ba da tabbaci ga matsayin tattalin arzikin kasuwannin kasar Sin sosai.
Ban da wannan kuma, Wen ya gabatar da jerin shawarwari domin tabbatar da hadin kai tsakaninsu, ciki har da fara yin shawarwari kan zubawa juna jari, hadin kai a fannonin zirga-zirga, samar da wutar lantarki, cigaban fannin sadarwa, da zurfafa hadin kai a fannin hada-hadar kudade, kasar Sin ta nuna maraba ga kamfanonin Turai da su yi amfani da kudin Sin RMB a cikin harkokin cinikayyarsu da hada-hadar zuba jari.
Kuma an ba da labari cewa, yau Juma'a 21 ga wata, firaminista Wen Jiabao ya kammala ziyararsa a Turai na tsawon kwanaki 2. Yanzu, ya dawo nan birnin Beijing.(Amina)