Sergio Ramos, dan wasan kungiyar Real Madrid ya bayyana cewa, mai horas da kungiyar wato José Mourinho ya zargi 'yan wasan kungiyar sosai. Amma a ganinsa, ba ma 'yan wasa ba, dukkan membobin kungiyar Real Madrid ya kamata su dauki alhakin duk wata nasara ko akasin haka a gasar da kungiyar ta bugu. Yanzu ba lokaci ne na yin bincike kan ko wane ne yake da laifi ko a'a, a ranar Talata kungiyar Real Madrid ta kara a gasar kungiyoyin wasan kwallon kafa ta zakarun nahiyar Turai tare da kungiyar Manchester City ta kasar Ingila.
Kana wani jami'in kungiyar Real Madrid ya ce, kungiyar ta sha kashi a wasan da ya gabata ba domin lamarin Cristiano Ronaldo ba. Ya kamata mu ci gaba da yin kokari wajen shiryawa wasannin gaba.(Zainab)