An ce, a ran 16 ga wata, firaministan kasar Japan Noda Yoshihiko ya bayyana wa 'yan jarida cewa, gwamnatin Japan bata ji dadi ba kuma tana bakin ciki kwarai ganin yadda ake zanga-zangar nuna kiyayya ga Japan a kasar Sin, don haka ya bukaci gwamnatin kasar Sin da ta dauki matakai domin hana cin zarafin hukumomi da mutanen kasar Japan da ake yi.
A game da zancen, a ran 17 ga wata a gun taron manema labaru da aka shirya, Hong Lei ya bayyana cewa, bai kamata kasar Japan ta dauki matakan kau da ido akan nauyin da ya rataya a wuyan ta ba, kana dukkan jama'ar kasar Sin ba su amince da sayen tsibirin Diaoyu da Japan tayi wanda bai dace da doka ba.
Dadin dadawa, Kakakin na kasar Sin ya nanata cewa, kamata ya yi Japan ta daina dukkan ayyukan keta ikon mallakar cikakken yanki na kasar Sin nan take, a kokarin daidaita wannan batu ta hanyar yin shawarwari a tsakaninsu kuma ana fatan Amurka za ta cika alkawarinta na cewa, ba za ta sa baki cikin batun tsibirin Diaoyu ba.
A gun taron manema labaru da aka shirya, wani dan jarida ya tambaya cewa, ministan tsaron kasar Amurka, Leon Panetta da ya fara kai ziyara kasar Sin ba da dadewa ba, ya bayyana cewa, yana fatan shi zai kasance mutum mai shiga tsakani kan batun tsibirin Diaoyu. Kafin wannan kuma, wani jami'in ma'aikatar tsaron kasar Amurka ya ce, ana iya yin amfani da yarjejeniya tabbatar da tsaro tsakanin Amurka da Japan kan batun tsibirin Diaoyu. To, mene ne ra'ayin kasar Sin kan wannan batu?
Hong ya amsa cewa, ba sau daya ba ne kasar Sin ta sha bayyana matsayin da ta dauka kan wannan yarjejeniya. Wato an rattaba hannu kan yarjejeniyar tabbatar da tsaro tsakanin Amurka da Japan a lokacin yakin cacar baki (wato cold war) bai kamata ta kawo illa ga moriyar bangare na uku ba, ciki har da kasar Sin.(Fatima)