Bisa labarin da Gidan Rediyon CRI ya samu, an ce, a ran 16 ga wata ne gwamnatin Somalia ta yi bikin mika mulkin kasa a Mogadishu, babban birnin kasar, hakan na bayyana cewa, sabon shugaban kasar Hassan Sheikh Mohamoud ya kama ragamar mulkin kasa a hukunce.
A yayin bikin, a cikin jawabinsa, shugaba Mohamoud ya sanar da cewa, muhimman ayyuka guda biyu da ke gabansa a cikin wa'adin aikinsa su ne, kyautata halin tsaron kasar da kuma bunkasa tattalin arzikin kasar. Ya kuma nuna cewa, gwamnatin dake karkashin jagorancinsa za ta yi shawarwarin lumana tare da shugabannin yankin Somaliland, ta yadda za a iya ciyar da dayantakar kasa gaba.
Shugaban kasar mai barin gado Sheikh Sharif Ahmed ya nuna goyon bayansa ga sabon shugaban kasar. Ya nuna cewa, zai ba da gudumawa ga bunkasuwar kasar Somalia a karkashin jagorancin sabon shugaban kasar.
A babban zaben kasar Somalia da aka yi a ran 10 ga watan Satumba, Hassan Sheikh Mohamoud ya sami goyon baya daga mambobin majalisar dokokin kasar wanda ya ba shi nasarar lashe babban zaben da yawan kuri'u 190 yayin da abokin takararsa ya samu yawan kuri'un 79. Mista Mohamoud ya zama shugaba na farko da majalisar dokokin kasar ta zaba tun cikin shekaru 21 da suka wuce. (Maryam)