Kasar Masar za ta amfani da ziyarar da shugaba Mohamed Morsi zai kawo a nan kasar Sin daga ranar 28 zuwa 30 ga watan Agusta, domin samun damar bunkasa cudanya tare da bangaren harkokin yawon bude ido na kasar Sin, ta yadda kasar Masar za ta kara yawan Sinawa 'yan yawon bude ido zuwa dubu 160 da za su kai ziyarar shakatawa a kasar Masar a shekarar 2013, in ji ministan kasar Masar dake kula da harkokin yawon bude ido Mohamed Hisham Zaazou a ranar Lahadi.
Kasar Masar ta karbi 'yan yawon bude ido daga kasar Sin dubu 110 a shekarar 2010, in ji mista ministan.
"Muna aiki tukuru domin ganin mun kara yawan masu yawon shakatawa daga kasar Sin zuwa dubu 160 a shekara mai zuwa ta hanyar maido da yarjejeniyar sufurin jiragen sama da kasashen biyu suka sanya wa hannu." in ji mista Zaazou da kamfanin dillancin labarai na kasar Masar MENA ya ruwaito kalamansa. (Maman Ada)