in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Kasar Masar ya fitar da sunayen sabon mataimakinsa da kuma sabbin shugabanni sojin
2012-08-13 11:00:06 cri
Shugaban kasar Masar Mohammed Morsi a jiya Lahadi ya nada Abdel Fatah el Seisy a matsayin ministan tsaron kasar da kuma shugaban rundunar koli na sojin kasar, in ji mai magana da yawun fadar shugaban kasar Yasser Ali.

El Seisy dan shekaru 58 da haihuwa ya taba kasancewa shugaban rundunar sojin dake kula da arewacin kasar sannan daga baya aka nada shi shugaban rundunar masu kula da leken asiri.

El Seisy zai maye gurbin Hussein Tantawi wanda da shi da tsohon babban hafsan sojin jiragen saman kasar Sami Enan aka umurce su da su yi ritaya daga mukaminsu.

Tsohon Alkali Mahmoud Mekki shi aka nada a matsayin Mataimakin Shugaban Kasar.

Hakazalika, Shugaba Morsi ya fitar da amincewarsa ga sabon kundin tsarin mulkin kasa inda ya soke nada da ke matsayi na wucin gadi da sojoji suka fitar a tsakiyar watan Yuni.

A cikin sabon kundin, idan majalissar dokokin wucin gadi ba su iya tsara ayyukansu cikin kwanaki 15 ba, shugaban kasar na iya nada wani sabo da za su iya wakiltar dukkan al'ummomi bayan ya tuntubi jami'iyyun siyasa don shirya wani kundin na sharan fage. (Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China