Wasikun masu sauraronmu
Bello Abubakar malam Gero a sokoto, tarayyar Nijeriya ya rubuto mana cewa, "A cikin shekarar 1971 ne kasar sin ta soma kulla huldar diplomasiya da kasashen duniya fiye da kasashe dari da saba'in da daya (171) cikinsu har da Nigeria, Niger, Cameroon, Kenya, Senegal, Ghana da dai sauransu. Wannan hulda tsakanin sin da nafiyar Afrika ta sami karbuwa tare da alfanu mai yawa ta fannoni daban-daban, kamarsu sha'anin siyasa, tattalin arziki, noma, gina masana'antu, kiwon lafiya, samar da ilmi, al'adu da makamantansu. Ba shakka kasar sin na bayar da kokarinta a kan nuna goyon baya ga dukkanin kasar da ke gudanar da tsarin mulki irin na demokuradiya, tare da bayar da gudunmuwa ta kowane fanni, tare da kare martabar diplomasiya tsakaninta da kasashen Afrika."
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku