Wata sanarwar da cibiyar ta bayar, wadda kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu, ta bayyana cewa, kwamitin tantance irin shuka na Najeriya ne ya bayyana nau'in farko na irin masara mai ingancin da ke kunshe da sinadarin Vitamin-A a ranar 4 ga watan Yulin shekara ta 2012, a matsayin Ife maizehyb 3 da kuma Ife maizehyb 4. An dauki wannan mataki ne da nufin magance matsalar karancin sinadarin Vitamin-A da ake fuskanta.
Sanarwar ta ce, cibiyar ta IITA tare da hadin gwiwar cibiyar nazari da samar da horo kan aikin gona (IAR&T) ne suka bunkasa irin masaran da ke kunshe da sinadarin na Vitamin-A.
Sauran cibiyoyin da ke cikin wannan hadin gwiwa a cewar sanarwar, sun hada da cibiyar binciken aikin gona da ke Zaria (IAR), jami'ar Maiduguri, cibiyar noman masara da alkama ta kasa da kasa (CIMMYT), jami'ar Illinois da jami'ar Wisconsin dukkansu a kasar Amurka.(Ibrahim)