in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kashi 55 cikin 100 na mutanen Mauritius na son yin kaura daga kasarsu, a cewar wani binciken jin ra'ayi
2012-07-23 11:08:56 cri
Kashi 55 cikin 100 na baligai a kasar Mauritius na fatan kaura, a cewar wani binciken jin ra'ayi da kamfanin Moriscopie ya gudanar a watan baya.

Wannan bincike na sanya ido kan halayyar jama'a, wanda aka yi kan mutane 924 ya nuna fargaba na mutanen kasar kan makomarsu, musamman matasa.

Binciken ya nuna cewa, kashi 84 cikin 100 na matasa masu shekaru 18 zuwa 24 na son ficewa daga kasarsu. Sai dai wannan fata na ja da baya tare da shekaru, duk da cewa ya cimma kashi 66 cikin 100 a wajen masu shekaru 25 zuwa 39, sannan kuma da kashi 47 cikin 100 a wajen masu shekaru 40 zuwa 59.

Bayan shekaru 60, kashi 26 cikin 100 na mutanen Mauritius na bukatar sake zaman rayuwarsu a wata kasa.

Jami'an da suka gudanar da binciken sun bayyana cewa, wannan cimma buri ba za a yi shi ta ko wane hali ba. Akasarin matasa, kimanin kashi 71 cikin 100 masu shekaru 18 zuwa 24 sun nuna cewa, suna son kaura amma ba ta ko wane hali ba.

A cewar darektar Moriscopie Brigitte Masson, wadannan alkaluma na nuna fargaba da rashin jin dadi na al'ummar Mauritius a gaban rashin tabbas na tattalin arziki.

"Wadannan alkaluma masu ta da hankali na shaida cewa, akwai shakku a game da makomar kasar ta Mauritius. Ana cikin halin kowa ya yi ta kansa dake nuna cewa, barin kasar ya fi alfanu. Abun na da kashin gaskiya idan an dubi yadda matasan da suka yi aure suke fuskantar matsalolin zaman rayuwa. Gidajen haya na da tsada haka ma kayayyakin gida suna da tsada ga masu dan karamin karfi." in ji madam Masson. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China