An rage farashin kayayyaki da kashi 25 cikin 100 a kasar Nijar albarkacin watan Ramadan
Manyan 'yan kasuwa dake Niamey babban birnin kasar Nijar sun dauki niyyar rage farashin duk wasu kayayyakin da aka fi bukata a tsawon wannan wata na Ramadan har zuwa kashi 25 cikin 100, domin tallafawa gwamnatin kasar kan ayyukan da take na kawo sauki ga matsalolin zaman rayuwa da mutanen kasar Nijar suke fuskanta. Ita dai wannan sanarwa an yi ta ranar Asabar a yayin wani bajen koli kayayyakin masarufi na musamman kan watan Ramadan da kungiyar 'yan kasuwa na babbar kasuwa dake birnin Niamey suka shirya a gaban ministan kasuwancin kasar malam Saley Saidou da kuma gwamnar da'irar birnin Niamey, madam Kane Aichatou.
"Wannan mataki ya biyo bayan kiran da hukumomin kasar suka yi, da kuma amsa tunanin aikata abubuwan alheri a cikin wannan wata mai daraja na Ramadan" in ji sakatare janar na kungiyar 'yan kasuwa na "Grand Marche" dake birnin Niamey. (Maman Ada)