in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron ministoci karo na 5 game da FOCAC
2012-07-19 14:07:17 cri

An bude taron ministoci karo na biyar game da dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, wato FOCAC a safiyar yau 19 ga wata , inda shugaban kasar Sin Hu Jintao da takwaransa na kasar Afrika ta kudu Jacob Zuma, da na kasar Benin Boni Yayi, da na kasar Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema Mbasogo, da na kasar Djibouti Ismail Omar Guelleh, da na Nijer Mahamadou Issoufou, da na kasar Cote D'Ivoire Alassane Dramane Ouattara, da kuma firaministocin kasar Cape Verde, José Maria Pereira Neves, da na kasar Kenya Raila Amollo Odinga, da babban sakataren MDD Ban Ki-Moon sun halarci taron.

Shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya yi jawabi kan batun zurfafa hadin gwiwa a tsakanin Sin da kasashen Afrika a yayin bikin bude taron inda ya kuma wakilci gwamnatin kasar Sin don sanar da sabbin matakan da Sin za ta dauka kan hadin kai tsakaninta da kasashen Afrika, wadanda suka shafi zuba jari, tattara kudi, ba da taimako, neman dunkulewar Afrika wuri daya, zaman lafiya da tsaro, yin mu'ammalar al'umma da kuma sauran fannoni.

A lokacin taron da za a shafe kwanaki biyu ana yinsa, ministocin dake kula da harkokin diplomasiya da hadin gwiwar tattalin arziki da suka fito daga kasar Sin da kasashe 50 na Afrika, da kuma shugaban kwamitin kungiyar AU za su tattauna kan muhimmin batu na bude sabon shafi kan sabuwar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare, kana da kimanta yadda aka aiwatar da matakai bayan taron ministoci karo na hudu da aka shirya a shekarar 2009, da kuma dudduba shirin ayyuka na Beijing daga shekarar 2013 zuwa 2015, don yin shiri kan hadin gwiwa a tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika a dukkan fannoni a shekaru uku masu zuwa.  (Bilkisu)
 

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China