in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattalin arzikin kasar Sin ya sami bunkasuwa yadda ya kamata a farkon rabin shekarar bana
2012-07-13 16:58:37 cri

A cikin farkon rabin shekarar bana, Sin ta aiwatar da manufar kudi mai kyau da ta kawo daidaituwar darajar kudi, tare kuma da kara kyautata manufofin kudin kasar dalilin da ya sa, tattalin arzikin kasar ya sami bunkasuwa yadda ya kamata.

Ran 13 ga wata, kakakin hukumar kididdigar ta kasar Sin Sheng Laiyun ya ba da bayyani kan yadda aka raya tattalin arzikin kasar Sin. A farkon rabin shekarar bana, yawan GDP da Sin ta samu ya kai kudin Sin Yuan biliyan 22709.8 wanda ya karu da kashi 7.8 cikin dari bisa na makamancin lokaci na bara.

Sheng Laiyun ya ce, a farkon rabin shekarar bana, sha'anin noma ya bunkasa sosai. An sake yin girbin hatsi mai armashi a yanayin zafi, kuma masana'antun kasar Sin sun sami bunkasuwa yadda ya kamata. Dadin dadawa, an sami bunkasuwa mai dorewa a fannin zuba jari domin samun kadarori. An dan samu ja da baya wajen zuba jari a fannin gidaje. Hakazalika, yawan karuwar farashin kayayyakin yau da kullum yana ta raguwa. Kuma, kudin da jama'a suka samu ya karu musamman ma a kyauyuka. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China