in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Palestinu za ta tono gawar Yasser Arafat domin binciken ainihin dalilin rasuwarsa
2012-07-06 12:34:45 cri

Kwamitin kula da aikin bincike kan dalilin rasuwar Yasser Arafat na Palestinu ya nuna cewa, a halin da ake ciki yanzu, ya riga ya kammala aikin share fage, muddin dai, an samu amincewa daga iyalan Yasser Arafat, to zai fara aikin bincike game da mutuwarsa. Kwamitin ya cigaba da cewa, kafin wannan, an riga an tarar da abin mamaki game da dalilin rasuwarsa, ba a cigaba da gudanar da aikin bincike ba saboda suna cikin mawuyancin hali. Amma yanzu, tun da gidan telibijin na Al Jazeera ya sanar da hakikanin sunan sinadari mai guba na Po-210 da aka samu a jikin kayan sa, hakan zai taimaka wajen binciken sosai, wanda zai sa a iya tabbatar da ainihin dalilin rasuwarsa ta hanyar binciken sinadari mai guba a cikin gawarsa, idan an cimma wannan burin, to, kwamitin zai yi kokarin kama masu lafuffukan da suka kashe Yasser Arafat, ko da yake, ana bukatar dogon lokacin kammala aikin. Ban da wannan kuma, kwamitin ya kara da cewa, samun sakamakon bincike ya fi muhummanci, shi ya sa, hukumar ikon al'ummar Palestinu, kungiyar 'yantar da Palestinu da kungiyar 'yantar da al'ummomin Palestinu wato Fatah za su yi hadin gwiwa tare da sauran jam'iyyu da kungiyoyi domin cimma burin yadda ya kamata.

Amma, bangaren Isra'ila ya nuna shakku kan sabon labarin da gidan telibijin Al Jazeera ya gabatar. A ranar 5 ga wannan wata, wani masanin da abin ya shafa na Isra'ila ya nuna cewa, ba mai yiyuwa ba ne a samu sinadarin Po-210 a cikin gawar Yasser Arafat bayan shekaru 8 da suka gabata da rasuwarsa, ya ce, irin wannan sinadari yana raguwa zuwa rabin adadinsa bayan kwanaki 138. Bisa sabon labarin da aka bayar, an ce, wani 'dan kimiyyar kasar Switzerland ya gano sinadarin Po-210 mai ingancin mBq 180 a cikin tsoffin kayayyakin da Yasser Arafat ya taba amfani da su, wanda yawansa ke da yawa. Amma, masanin Isra'ila ya nuna cewa, idan an kashe Yasser Arafat ta hanyar yin amfani da irin wannan siandarin Po-210, bai kamata ba a tarar da sauran sinadarin mai ingancin haka ba bayan shekaru 8 da suka wuce, idan kuma hakan ya faru, to, sai dai ya kasance sabon sinadarin guba da aka sanya a kan gawarsa, wato bayan rasuwarsa, amma ba dalilin da ya janyo rasuwarsa ba ke nan.

Ya ce, idan sinadari mai guba yana kasancewa kan wadannan kayayyakin da matar Yasser Arafat Suha Arafat ta ajiye, me ya sa Suha Arafat ita kanta ba ta kamu da ciwo ba a cikin shekaru 8 da suka gabata? Ban da wannan kuma, me ya sa Suha Arafat da hukumar ikon al'ummar Palestinu ba su yarda da asibitin kasar Faransa inda Yasser Arafat ya kwanta ya sanar da yanayin ciwonsa ba bayan rasuwarsa? Kuma a wancan lokaci, babu alamar da ta nuna cewa, Yasser Arafat ya gamu da sinadari mai guba kafin rasuwarsa.

Abin da ya fi jawo hankali shi ne ganin yadda wassu al'ummomin kasashen duniya suna goyon baya ga aikin sake binciken dalilin rasuwar Yasser Arafat. A ranar 5 ga wannan wata, kasar Tunisiya ta yi kira ga kungiyar tarayyar kasashen Larabawa da ta shirya taron gaggawa domin tattauna ainihin dalilin rasuwar Arafat. A wannan rana, ministan harkokin wajen kasar Rafik Abdessalem ya gaya wa manema labarai cewa, Tunisiya ta yi kira ga kungiyar tarayyar kasashen Larabawa da ta yi taro cikin gaggawa, sannan, ya kamata a kafa wani kwamitin kasa da kasa domin binciken dalilin rasuwarsa. Daga baya, kungiyar tarayyar kasashen Larabawa ta gaskanta cewa, ta riga ta samu rahoton da wakilin Tunisiya ya gabatar game da kira taron ministoci domin nazarin dalilin rasuwar Arafat. Yanzu, kungiyar ta riga ta aika wa kasashe mambobinta rokon kiran taron, ta yadda za a tsai da kudurin taimakawa aikin da bangaren Palestinu zai gudana kan batun.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China