in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta cimma nasarar mallakar fasahohi mafi muhimmanci uku a bangaren zirga-zirgar kumbo mai dauke da mutane
2012-06-29 16:56:26 cri

Shugaban ofishin kula da harkokin zirga-zirgar kumbo mai dauke da mutane na kasar Sin Wang Zhaoyao ya bayyana a nan birnin Beijing a ran 29 ga wata cewa, yanzu Sin ta mallaki fasahohi mafi muhimmanci uku a bangaren zirga-zirgar kumbo dake dauke da mutane.

A gun taron manema labaru da aka yi a wannan rana, Wang Zhaoyao ya ce, Sin ta gudanar da wannan aiki har na tsawo shekaru 20. Baitulmalin gwamnatin tsakiya na kasar Sin ya kebe kudi Yuan biliyan 39 a wannan fanni. Ya ce, bayan ayyukan gwaje-gwaje har sau 10 da aka yi, yanzu Sin ta cimma nasarar mallakar muhimman fasahohi uku da ya kunshi harba kumbon da ke dauke da mutane da dawo da shi doron kasa, 'yan sama jannati sun fito daga kumbon lami lafiya,sannan da fasahar hada kumbuna biyu waje guda. Wadanda kuma suke inganta muhimman kayayyakin zirga-zirgar samaniya tare kuma da kara karfi a wannan fanni, har ma da kara azama ga nazarin da ake yi a sauran fannonin da abin ya shafe.

Hakazalika, Wang Zhaoyao ya ce, Sin za ta ci gaba da hadin gwiwa da kasashen waje a wannan fanni ta fuskar kimiyya, koyar da juna da horar da 'yan sama jannati da sauransu.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China