Bayan da kumbo Shenzhou-9 ya kammala aikinsa kuma ya dawo nan doron kasa yadda ya kamata. Kafofin yada labaru na kasa da kasa sun ba da labaru nan take, tare da nuna babban yabo ga aikin da Sin ta yi.
Shafin Intanet na kafar yada labaru ta CNN ta kasar Amurka ya ba da labari cewa,kumbon Shenzhou-9 ya dawo doron kasa lami lafiya, wanda ya kammala wasu manyan ayyuka da dama. Kuma Sin ta zama kasa ta uku a duniya da ta kware wajen gudanar da aikin hade kunbuna a sararin samaniya dake dauke da mutane da kanta bayan Amurka da Rasha.
Kafar yada labaru ta ITAR ta kasar Rasha ta mai da hankali sosai kan aikin da Sin ta yi, wadda kuma ta ba da labaru kan dukkan ayyukan da kumbon Shenzhou-9 ya yi, tare kuma da waiwayi wasu muhimman ci gaba da Sin ta samu a wannan fanni.(Amina)