Jamhuriyyar Nijar, kasa ce dake cikin yankin Sahel, da fadinta ya kai murabu'in kilomita miliyan guda da dubu dari biyu da sittin da bakwai, da kuma kashi 62 cikin 100 na al'ummarta ke rayuwa cikin talauci, da ta dade a tsawon shekaru aru aru tana fama da matsalar karancin abinci jefi jefi, matsalar dake da nasaba musammun ma da rashin ruwan sama, fari mai tsanani da kuma kwari dake lalata albarkatun noma. A cikin wannan shekara, kasar Nijar na da gibin abinci dake da nasaba da rashin damana mai kyau a cikin shekarar da ta gabata wanda ya kai fiye da tan dubu 690, lamarin da ya janyo mutane miliyan 5.4 na wasu yankunan kasar fadawa cikin kangin yunwa da kuma matsalar karancin abinci. Domin fuskantar wannan kalubale, da kuma shirya wa damanar shekarar 2012 zuwa 2013, gwamnatin kasar Nijar a karkashin ma'aikatar hasashen yanayi ta kasa ta ba da albishir mai kyau inda ta bayyana cewa damanar bana za ta fi ta bara kyau bisa ga ruwan sama da za'a samu, haka kuma hukumomin kasar sun sanya dukkan matakan da suka wajaba domin samun damana mai albarka. A game da haka ne gwamnatin kasar tare da kasashe da kungiyoyi masu tallafawa kasar, ta samar da tan fiye da 7220 na irin shuka mai inganci zuwa ga mutanen dake kauyukan da suka samu gibin abinci, bisa bukatun da aka kiyasta a wannan shekara ga tan 9642 a kan jimillar kudin Sefa biliyan 6,107 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 11.4, a cewar cibiyar kula da watsawa da shigar da fasahohin zamani ta ofishin ministan noma.
Irin shuka da aka samar sun hada da hatsi, dawa da wake da suka kasance muhimman abincin da aka fi nomawa da ci a cikin kasar. Kuma wadannan iri zuwa taimakawa wajen noma fiye da kadada miliyan 1.2 tsakanin manoma dubu 830 da aka rarraba a tsakanin yankuna 200 da suka fi fuskantar karancin abinci a cikin kasar. Domin kare albarkatun noma daga kwari da makamantan haka, gwamnatin Nijar, ta hanyar babban ofishin kula da kare albarkatun noma na DGPV, na shirin kara karfinsa da ayyukansa a wannan shekara wajen gudanar da aikinsa na watsa maganin kwari a dukkan fadin kasar. Inda a yanzu haka ake da fiye da lita dubu 60 na maganin kwari, sannan ana jiran karin wasu fiye da lita dubu 40, lamarin da zai taimaka wajen kulawa da gonaki ekta dubu 400 bisa dubu 130 a shekarar da ta gabata.
Haka kuma ofishin DGPV ya tanadi kayayyaki iri daban daban masu inganci da dama domin gudanar da aikinsa yadda ya kamata a kasa ko a sama.
Hakazalika gwamnatin kasar Nijar, duk bisa hanyar yin rigakafi da kuma matakan da ta dauka domin samun damana mai albarka a wannan shekara ta bayyana cewa taimakon kungiyoyi da kasashe a wannan fanni na da muhimmancin gaske, dalilin haka, idan gwamnatin Nijar tana da rauni wajen magance wannan matsala ta karancin abinci take yin kira ga kungiyoyin bada tallafi.
Wannan ya sa tun lokaci ta samu labari, kan barazanar kwari da fari a yankin arewacin kasar kuma a lokacin da aka soma aikin damana, hukumomin kasar Nijar suka mika kira ga gamayyar kasa da kasa na bukatar taimako domin fuskantar wannan annoba ta kwari da fari. (Maman Ada)