Kumbon 'yan sama jannati mai dauke da Sinawa zai hadu da tashar Tiangong mai lamba daya dake cikin sararin samaniya a tsakiyar watan Yuni
Kakakin ofishin kula da harkokin kumbunan 'yan sama jannati masu dauke da mutane na kasar Sin ya sanar a ranar Asabar 9 ga wannan wata, cewar an isar da kumbon 'yan sama jannati mai lamba 9 kirar Shenzhou wanda zai hadu da tashar Tiangong mai lamba daya dake cikin sararin sama da rokit da za a yi amfani da shi domin harba wannan kumbon zuwa sararin samaniya a yankin da za a harba shi daga yankin hada su tare, dake cibiyar harba taurarin dan Adam ta Jiuquan dake arewa maso yammancin kasar Sin. Wannan ya alamta cewa, an riga an shiga lokacin karshe na harba kumbon mai dauke da 'yan sama jannati zuwa sararin sama domin haduwa da tashar Tiangong mai lamba daya.
Bisa shirin da aka tsara, za a zabi wani lokacin da ya dace a tsakiyar watan Yunin da muke ciki domin harba wannan kumbo mai lamba 9 kirar Shenzhou.
Kakakin ya kara da cewa, yanzu 'yan sama jannati wadanda za su dauki wannan kumbon kirar Shenzou sun riga sun samu cikakken horaswa da gwaje-gwaje a doron duniya, kuma suna cikin koshin lafiya yanzu. (Sanusi Chen)