Makasudin wannan taro na kwanaki hudu shi ne samar da hanyoyin bunkasa tsarin aiki da maganar shiga kungiya ga ma'aikatan kasa dake gudanar da aikin bada jini, likitanci da makamantan haka.
Kungiyoyi masu zaman kansu da masu shirya samar da taimakon bada jini, suna iya kafa wani kawance tare da sauran kungiyoyi a wannan fannin dake cikin wasu kasashe.
Hakazalika, dandalin zai taimaka ga yin musanyar fasahohi da labarai kan batutuwan dake da nasaba da aikin bada jini da tsaron jini. Haka ma za'a tattaunawa kan wasu batutuwan da suka shafi kyautatuwar gidajen likita da kiyaye aikin bada jini, ayyukan da aka yi da kuma wanda za a yi a gaba, wato aikin bada jini a Afrika, da tabbatar da ingancin jini daga mutanen da suka bada.
A cikin jawabinsa na bude taron, ministan kiwon lafiya na kasar Mauritius, Lormus Bundhoo ya tunatar da cewa, koda yake likitanci kan aikin bada jini ya samu sauye sauye ta fuskar kiyayewa da inganci, kulawa da tsaron aikin bada jini ya samu cigaba, amma har wannan fanni na janyo hankali. (Maman Ada)