A cewar wadanda suka tsara, wannan dandali na farko kan yara kanana a kasar Guinea na da manufar samar da wani tsarin tattaunawa da yin musanya, kan wasu matsalolin dake da nasaba da "rayuwa da kare al'ummar" kananan yara, da aka gano daga cikin al'ummomin dake da rauni a cikin kasar.
Kasar Guinea ta sanya hannu kan dokokin kare kananan yara a shekarar 1990, sannan kuma ta kebe watan Yuni a matsayin watan kananan yara a cikin kasar, a lokacin da ake shirin bikin ranar kananan yara ta duniya, in ji ministar kasar Madam Nantenin Cherif.
Bisa wannan manufa, gwamnatin kasar Guinea da kuma kungiyoyin kasashen waje dake bada tallafi sun dauki niyyar maida hankali kan ilmim kananan yara, bada kariya da yara, kare yara daga aikin karfi da cin zarafinsu, lafiyar kananan yara, shari'ar kananan yara da kuma matsalolin dake nasaba da makomar yara marayu da yaran da uwayensu suka yi watsi da su.
A cikin jawabinsa zuwa ga mahalarta taron, shugaban majalisar kananan yara ta kasar Guinea ya bayyana cewa, kudaden da ake kebewa sha'anin kananan yara sun yi kadan, kashi 1.4 cikin 100 bisa ga na kasafin kudin kasar baki daya, dalilin dake sanya wasu yaran kasar su rasa samun kulawa a fannin kiwon lafiya, ilmi da samun abinci mai gina jiki. (Maman Ada)