Hukumomin sun jaddada cewa, wannan tawaga ta kasance ta wucin gadi, sabili da za a ci gaba da kara sunayen 'yan wasa kafin karshen watan Yuni, inda za a tsaida jerin sunayen 'yan wasa na dindindin
A cikin jerin sunayen 'yan wasa na wucin gadi, akwai Cameron Van der Burgh, wanda ya samu lambar tagulla cikin gasar fid da gwani ta duniya a fannin iyo, da tarmamuwa mai tashe wato Chad le Clos, da kuma Roland Schoeman wanda ya sha samun lambobi ta bangaren iyo za su halarci wasannin Olympic.
A bangaren gudu kuma, akwai Cornel Fredericks da kuma LJ van Zyl, masu gudun mita 400. Akwai kuma Caster Semenya mai lambar tagulla ta duniya wajen gudun mita 800, da kuma Sunette Viljoen mai rike da matsayin bajimta na jefa mashi na duniya.
Ta bangaren gudun famfalaki, a sashen maza, akwai 'yan gudu guda 3 da suka hada da Lusapho April, Stephen Mokoka da kuma Coolboy Ngamole. Ta bangeren mata kuma akwai Rene Khalmer, Tanith Maxwell, da Irvette van Blerk.(Abdou Halilou)