Eden ya kasance dan wasa mafi samun daraja wato MVP na gasar Ligue 1 ta kasar Faransa a kakar wasa ta 2011-2012, wanda ke samun karbuwa sosai a nahiyar Turai. Bayan da ya shiga kungiyar Chelsea, zai zama MVP din gasar Ligue 1 na 4 da kungiyar ta yi kokarin kwato su. Don haka, lamarin ya sa ake sanya ayar tambaya cewa, me ya sa kungiyar Chelsea ke son neman kwararun 'yan wasa daga gasar L1?
To, kafin mu amsa wannan tambaya, ya kamata mu mai da hanakali kan tarihin dan wasan nan, wato Eden Hazard, domin mutumin yana janyo hankali sosai yanzu. An haife shi a kasar Belgium a shekarar 1991. A lokacin da yake da shekaru 10 da haihuwa, masu kula da aikin neman 'yan wasa na kunigyar Lille sun gano fasahar da ta nuna cewa ya na da kuzari, don haka an shigar da shi cikin kungiyar a shekarar 2006. Zuwa shekarar 2008, Eden dake da shekaru 17 a lokacin ya fara buga kwallo cikin raga a manyan wasannin da aka shirya a karkashin tsarin Ligue 1.
A kakar wasanni ta 2011-2012 da ta gabata, Eden ya sanya kwallaye 20 cikin raga, tare da taimakawa samun maki guda 15. Wadannan nasarorin da ya samu sun taimakawa kungiyarsa ta Lille wajen samun damar shiga cikin babbar gasar da ke gudana a tsakanin zakarun kasashen Turai, wato UEFA CHAMPIONS LEAGUE, haka kuma suka sanya Eden ya zama MVP din tsarin gasar Ligue 1 a karo na 2.
Duk da cewa, shekarunsa 21 ne kawai, amma Eden ya iya gudu tare da kwallo cikin sauri, kana yana da kwarewa sosai wajen neman damar samun maki a wajen wasa. Yadda yake da fasahohi wajen taka leda ya sa wasu sanannan masu horar da 'yan wasa suke yabashi sossai, har ma suna neman jawoshi su sanya shi cikin kungiyoyinsu. Amma kungiyar Chelsea ita ta yi sa'a wajen samun Eden a karshe.
Kungiyar Chelsea dai, gaskiya tana son samun 'yan wasa masu matsayin MVP na tsarin gasar Ligue 1, ganin yadda ta riga ta samu 'yan wasan irinsu har guda 3, wadanda su ne Didier Drogba, Mickael Essien, da Florent Malouda.
Wannan ya sheda wata manufar da kungiyar Chelsea take da ita , wato bata so ta yi amfani da kudinta wajen samun wasu fitattun 'yan wasa da suka yi suna sosai a duniya, a maimakon haka, ta fi so ta zabi wasu kwararrun 'yan wasa da suka yi suna a cikin wasu tsarin gasanni da ba su da cikakken tasiri a duniya. Ga misali, tsarin gasar Ligue 1.
Wannan manufa ta sanya kungiyar ta samu kwararrun 'yan wasa da yawa kamarsu Didier Drogba, Mickel Essein, Florent Malouda, Lassana Diarra, da Eden Hazard, da dai sauransu, wadanda akasarinsu sukan taimakawa kungiyar wajen kara karfinta.
Kudin da kungiyar Chelsea ta kashe wajen samun wadannan kwararrun 'yan wasa ya kai kudin ingla fan miliyan 110. Sai dai kamar yadda malam bahaushe ke cewa,"kwaliya ta biya kudin sabulu har da na mai, da kwalli". Yadda kungiyar ta kashe makudan kudi wajen neman samun wasu 'yan wasa da suka fara yin suna, ya sanya kungiyar ta samu nasarori da yawa a shekaru 8 da suka wuce, inda ta kasance zakaran Premier League har sau 3, da zama zakaran babbar gasar neman cin kwofin FA ta kasar Birtaniya har sau 4, har ma cimma nasara a wajen zaman zakara a gasar UEFA CHAMPIONS LEAGUE.
Amma babu shakka, kungiyar Chelsea ba za ta yi nasara kamar haka ba, in ba ta tare da kwararrun 'yan wasan da ta samu daga tsarin gasar Ligue 1 ta kasar Faransa. Kuma dalilin da ya sa kungiyar ta fi son ta zabi 'yan wasan daga L1, shi ne domin kungiyoyin kasar Faransa suna da kwarewa sosai wajen horar da 'yan wasa ta bangaren matasa.
Ga misalin, kungiyar Lille da Eden Harrade ke ciki, wanda ta kan rasa wasu kwararrun 'yan wasa a ko wace shekara, domin wasu manyan kungiyoyi masu kudi na ta kokarin kwace 'yan wasan daga hannunta. Amma a shekarun baya, kungiyar ba ta taba gamuwa da koma baya ba, domin a ko wace shekara ta kan iya sanya wasu 'yan wasa matasa suka fara taka kwallo a madadinta. Ta wannan misali za mu iya ganin kwarewar kungiyoyin kasashen Faransa wajen gano matasa masu fasaha tare da horar da su.
Ban da haka kuma, kasar Faransa tana kusa da nahiyar Afirka, kana jama'ar kasashen ahiyar Afirka da dama suna magana da yaren Faransanci. Don haka, akwai 'yan wasa 'yan asalin kasashen Afirka da suka je kasar Faransa don neman samun ayyukan yi da ilimi. Hakan ya sa kasar Faransa ke iya samun wasu 'yan wasan Afirka masu kwazo da kuzari.
A lokacin da aka gudanar da wasar neman cin kofin Afirka a shekarar 2012, 'yan wasa 46 dake taka leda a tsari gasar L1 na kasar Faransa sun koma kasashensu na asali dake Afirka domin shiga gasar. Hakan ya shaida yadda kasar Faransa take samun kwararrun 'yan wasa da yawa daga Afirka.(Bello Wang)