An bude taron watsa labaru da sadarwa na kasashen Afrika a ranar 4 ga wannan wata a birnin Cape Town na kasar Afrika ta kudu. Ministar sadarwa ta kasar Afrika ta kudu ta bayyana cewa, nahiyar Afrika na da babbar kasuwar watsa labaru da sadarwa, kuma ta kasance kamar wani babban wurin hakon zinariya a idanun 'yan kasuwa na sadarwa.
Ministar sadarwa ta kasar Afrika ta kudu, ta yi jawabi a gun bikin bude taron inda ta ce, nahiyar Afrika na da mutane biliyan daya, amma wasu daga cikinsu ba su ci gajiyar bunkasar sadarwa ta zamani, sabili da hakan, Afrika ta kasance kasuwa mafi girma ta duniya da ya kamata a ci gaba da raya ta. Ta kuma yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su kara zuba jari ga kasashen Afrika da sayar da fasahohi gare su, domin taimaka musu wajen samu bunkasuwa tare da sauran kasashen duniya. Ta kuma kara da cewa, za a tattaunawa cikin gaggawa kan yadda za a tabbatar da yarjejeniyoyin hadin gwiwa a fannonin sanarwa da watsa labaru da kasashen Afrika suka kulla, domin kafa tsarin sadarwa da ya hada birane da kauyuka.
Taron watsa labaru da sadarwa na Afrika zai shafe kwanaki 4, wakilan kasashen Afrika da kasashe daban daban na duniya za su tattauna yadda za a raya kasuwar sadarwa a Afrika.(Lami)