A ranar 4 ga wannan wata, firayin ministan kasar Kongo(Kinshasa) Matata Pony ya sanar a birnin Kinshasa cewa, gwamnatin kasar ta tsaida kudurin buga takardun kudi masu yawan daraja a kasar, darajar sabbin takardun kudi na kasar zai hada da Franc na Kongo 1000, 1500 da 2000.
Firayin minista Matata Pony ya nuna cewa, za a fara amfani da wadannan takardun kudi ne daga ranar 2 ga watan Yuli mai zuwa saboda ana son tabbatar da zaman karko na tattalin arzikin kasar bisa manyan tsare-tsare tare da hana raguwar darajar kudin Franc na Kongo, hakan zai taimaka wajen amfani da sabbin takardun kudi a kasuwanni yadda ya kamata.
Yanzu, ana amfani da takardun kudi masu darajar Franc na Kongo 100, 200 da 500 a kasar Kongo(Kinshasa). Kididdigar babban bankin kasar ta nuna cewa, a halin da ake ciki, darajar dalar Amurka guda ta yi daidai da Franc na Kongo 924. A cikin shekaru 2 da suka gabata, darajar kudin musanya tsakaninsu ba ta sauya bisa babban mataki ba, amma, ana nuna damuwar raguwar darajar kudin kasar.(Jamila)