A gun taron manema labarai da majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta shirya a wannan rana, Liu Tuo ya ce, daga shekarar 1992, kasar Sin ta kan zuba biliyoyin daloli a kowace shekara ta bangaren hana lalacewar gonaki da yaduwar hamada. Baya ga haka, ta kuma kafa wani tsarin damawa da al'umma. A sa'i daya, kasar Sin ta inganta hadin gwiwa da gamayyar kasa da kasa, abin da ya taimaka sosai wajen hana yaduwar hamada a kasar Sin tare da kara samun kudin shiga ga manoma.(Lubabatu)