Saurin karuwar jimillar kudin cinikin waje da jihar Tibet ta samu a farkon bana ya kai matsayin gaba a duk kasar Sin
Bisa kididdigar da hukumar kwastan nta birnin Lhasa ya bayar a kwanan baya, an nuna cewa, jimillar kudin cinikin waje da jihar Tibet ta samu ta kai dalar Amurka miliyan 460 a watanni hudu na farkon shekarar da muke ciki, wato ta karu da kashi 117 cikin kashi dari idan aka kwatanta ta da na makamancin lokacin bara, hakan kuma karuwarta ta kai matsayin gaba a duk kasar Sin.
Bisa kididdigar da aka bayar an ce, jihar Tibet na mayar da hankali kan kananan cinikin da aka yi a kan da kasashen waje, wadanda kayayyakin suka hada da na sake-sake, injuna da na lantarki, kuma amfanin gona da dai sauransu. Muhimman abokan jihar wajen cinikin waje sun hada da kasashen Nepal, Amurka, Netherland da dai sauransu. (Bilkisu)