Bisa kididdigar da hukumar kidaya ta kasar Sin ta fitar, an ce, tun daga shekarar 2003 zuwa ta 2011, matsakaicin saurin karuwar tattalin arzikin kasar Sin a kowace shekara ya kai kashi 10.7 cikin kashi dari, a yayin da matsakaicin saurin karuwar tattalin arzikin kasa da kasa ya kai kashi 3.9 cikin dari. Sannan, a shekarar 2002, yawan tattalin arzikin kasar Sin ya kai kashi 4.4 cikin kashi dari bisa na jimillar tattalin arzikin dukkan kasashen duniya, amma ya zuwa shekarar 2011, wannan adadi ya kai kashi 10 cikin kashi dari. Bugu da kari, tattalin arzikin kasar Sin ya kai matsayi na biyu a duniya yanzu.
Amma matsakaicin yawan GDP na kasar Sin ya kai kimanin matsayi na 90 kawai a duk duniya sakamakon yawan dimbin mutanenta. Sabili da haka, har yanzu kasar Sin kasa ce mai tasowa. (Sanusi Chen)