A cewar Mista Han, zuwa yanzu an riga an tabbatar da yanayin da ake ciki dangane da aikin samar da hatsi a nan kasar Sin, inda fadin filayen gona da aka yi amfani da su wajen shuka hatsi ya karu sosai. Kamar yadda ake hasashen cewa, fadin ya kai kadada miliyan 28, wanda ya karu da kadada dubu 132 idan an kwatanta da na bara. Haka kuma a galibin yankunan da ake shukar hatsi ana samun karuwa wajen yawan samar da hatsi.
Han ya kara da cewa, yadda za a samar da hatsi da yawa zai taimaka ga aikin raya tattalin arzikin kasar Sin, haka kuma zai taka muhimmiyar rawa a fannonin tabbatar da biyan bukatun da ake da su a kasuwannin kasar, kiyaye farashin kayayyaki, kyautata zaman rayuwar jama'a, da kara jituwa a tsakanin al'umma. (Bello Wang)